By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum daya tare da kona Sakatariyar karamar hukumar Nnewi ta Kudu dake Ukpor jihar Anambra.
DUBA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: Masu Garkuwa Da Mutane Sun Mamaye Fadar Sarkin Abuja Sunyi Awon Gaba Da Basaraken
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis. Shaidun gani da ido sun ce marigayin yana daya daga cikin jami’an tsaro a Sakatariyar Majalisar karamar hukumar.
Tashin hankalin ya dabaibaye majalisar tare da fargabar rayukan mazauna yankin.
Ukpor da ke Nnewi ta Kudu karamar hukuma ce ta wasu fitattun ‘yan siyasa, ciki har da ministan sufurin jiragen sama na farko, Mbazulike Amechi, mai shekaru 92; tsohon dan majalisar wakilai, Hon Cyril Maduabom da tsohuwar kakakin majalisar Anambra Hon Rita Maduagwu da dai sauransu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan Anambra, Ikenga Tochukwu, ya ce har yanzu bai tantance adadin wadanda suka mutu ba.
Ya ce an tura jami’an tsaro yankin yayin da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar ke can a kasa domin kashe gobarar.
Tochukwu ya ci gaba da cewa kwamishinan ‘yan sandan Anambra ya je wurin da lamarin ya faru domin tantance ma kansa.
Inda ya ce wannan lamarin na sanya wuta ne da wasu bata gari suka yi.