By Abbas Yakubu Yaura
An yi awon gaba da basaraken al’ummar Bukpe da ke karamar hukumar Kwali a babban birnin tarayya Abuja, mai martaba Alhaji Hassan Shamidozhi.
DUBA WANNAN LABARIN: Bankin Duniya Ya Dakatar Da Wani Kamfani Na Najeriya Saboda Karbar Rashawa
Dan’uwan sarkin, wanda shi ne Babban Limamin Babban Masallacin Al’ummar garin, Malam Jibrin D.Gimba, ya tabbatar wa Jaridar Daily Trust faruwar lamarin.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:32 na daren ranar Laraba.
Ya ce sarkin da ke zaune a kofar fadarsa yana shan iska, an yi masa harbi da bindiga.
“Na shiga gidana ne bayan ya bar fadarsa sa’ad da ya ce yana so ya yi wanka bayan haka zai fito ya huta a gaban fadarsa don ya sha iska mai kyau,” in ji ɗan’uwan.
“Bayan ‘yan mintoci kaɗan, na fara jin karar harbe-harbe… Na leƙa ta taga na kuma gano cewa masu satar mutane ne sun yi awon gaba da shi.”
Gimba, ya ce wadanda suka yi garkuwa da sarkin ba su yi wata hulda da dangin ba, ya ce harin shi ne na uku a cikin al’ummar.
Sannan ya ce sa’o’i bayan sace shi, wasu ‘yan sanda sun ziyarci unguwar amma daga baya suka fice.
Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, bata amsa tambayoyin wakilinmu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Tun da safiyar ranar Alhamis din nan, an ga masu jaje a fadar sarkin gargajiyar da aka sace suna kaiwa da komowa.
Comments 1