Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu Matasa biyu yan uwan juna, a garin Rigachikun dake karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da musalin karfe 12:45 na safiyar yau Alhamis a yankin Tsallake Dogo dake darin garin Rigachikun.
Rahotanni sun nuna cewa, Yan bindigan sun yi ta yin harbi kan Mai uwa da wabi, domin tsoratar da mazauna yankin kafin su shiga inda lamarin ya afku.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kaduna ta sanar da ranar koma wa makarantu a jihar
Wani mazaunin yankin Mai suna Mohammed Awalu ya bayyana cewa, lamarin ya yi matukar firgita al’umar yankin duba da cewa, Matasa ne Yan bindigan suka sace
Kazalika ya kuma ce, Rabon da yan bindiga su farmaki yankin, tun a shekarar da ta gabata.
Ko da aka tuntumi jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kaduna ASP Jalige Mohammed ya ce, ya na cikin wani taro, Amma zai binciki Karin bayani kan lamarin.