Jimami na aukuwar wani lamari ya karade kauyen Jangeme dake Gusau a Jahar Zamfara, inda yara goma suka mutu bayan cin tuwo. Kamar yadda Jaridar Dailytrust ta wallafa a shafinta
Yaran sun rasa rayukansu su daya bayan daya sanadiyyar Ziyarar da gwagwgwansu ta kawo musu, inda ta dafa musu tuwo da guba a ciki.
A yadda aka ruwaito, bayan zuwan gwagwgwansu, ta fara tsince tsakuwa daga cikin masarar, sai ta kai nika, bayan ta dawo ashe da akwai bera da ya mutu bayan ya ci magani, sai ta shanya kamin ta fara girkin.
Shugaban Majalissar Dokokin Kaduna ya halarci Sallar Idi a Rigachikun
Abdullahi Bello Baban yaran, cewa yayi bayan sun kammala cin abincin gaba daya gidan kowa ya shiga matsala, yaran suka kama mutuwa daya bayan daya.
Abdullahi Bello yace in banda shi da matarsa babu wanda ya rage, sauran duk sun rasu.
Yace “ba karamin tashin hankali bane a ce, a cikin iyali daya, ayi irin wannan gagarumar rashi, ban iya bacci ba da abun ya auku, Matata nan take ta sume aka kaita asibitin, gaskiya abun zai dade yana damunmu.”
“Biyu dai daga cikin yaran, munyi kokarin kaisu asibitin dake Gusau amma sun mutu a can, bayan mun dawo da su muna rufe su, nan take naji kira wasu guda uku sun sake mutuwa, ciki hadda kanwata wadda ta dafa abincin, wanda ya kama yara na goma tare da kanwata suka rasa rayukansu.”
Babu abunda muka iya sai dai mu mikama Allah al’amarin.
Mai rahotanmu cewa yayi akwai yaro mai kimanin shekaru sha daya mai suna Sadiq, shi ya rasu bayan kanaki kadan a babban asibitin dake garin Gusau, wanda shine cikon na goma wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar cin tuwon.