Duk cikin shagulgulan Sallah, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Jahar Kano ya sallami fursinoni dari da talatin da shida daga gidan gyaran hali daban-daban, sannan ya ba su dubu biyar-biyar a matsayin kudin mota izuwa gidajen su.
Bayan kammala raba musu kudaden, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gargade su da su zama mutane masu dabi’u na gari, su zama masu taimakawa Yan uwansu da garuruwan su. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Yace ” a matsayinku na Yan Najeriya, suwaye ya kamata ku dauki nauyin su, gamu munzu a ranar Sallah don mu fidda ku, an yafe muku.”
Ya bayyana hakane lokacin da ya kai ziya gidan gyaran hali dake Gorondutse.
KARANTA:- Ku taimaka ku sa baki a saki Nnamdi Kanu, Kalaman Ƙungiyar Ohanaeze ga gwamnonin Kudu
Mu zo muga ya ya kuke, sannan mu taya ku murna, muna fatan wadanda suka tuba za su rike alkawari ba za su koma kan miyagun ayyukansu ba na baya.
Ganduje ya cigaba da cewa, wadan sunku an sake su ne saboda rashin lafiya, wadan sunku kuma sun dade a nan, wadan sunku kuma sun tsaya anan saboda sun kasa biyan kudin tarar da aka dora akansu.
Yace wannan yafiya da aka yi maku na daga cikin alfarmar shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya bada umarnin ziyartar gidan gyaran hali daban-daban don yin hakan.
Ya kara da cewa muna bin wannan tsari ne kamar yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin haka, duba da yadda cutar Covid-19 ta yi kamari.
Suleiman T. Suleiman shugaban gidan gyaran hali, lokacin da yake bayani cewa yayi “Ina yabawa gwamna Ganduje kan irin tausayawa mazauna gidan gyaran hali, da kuma sanya wannan gidan a daya daga cikin gidan da ya ziyarta.”
Ya cigaba da cewa “Nayi ayiki sama da shekaru 30 a gidan gyaran hali daban-daban a fadin kasar nan, amma banga inda gwamnan Jahar yake nuna so da kauna ga Yan gidan gyaran hali ba irin Dakta Abdullahi Umar Ganduje.”
Kamar yadda Sulaiman T. Sulaiman ya bayyana, yace gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kawo ziyara a lokacin karamar Sallah, Kwana saba’in da suka gabata kenan, inda nanma ya sallami fursinoni dari da talatin da shida.
Suleiman T. Suleiman ya kara yabawa gwamna Ganduje bisa jiyar da Yan gidan gyaran hali dadi ta yadda ya saya musu Raguna da awaki don yin shagalin Sallah.