Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya musanta rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka yada da ke nuni da cewa ya canja ra’ayinsa kan alkawarin da ya dauka na cewa ba zai daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke kan dan takarar jam’iyyar APC na jihar Yobe ta Arewa ba a zaben 2023 ba,kamar yadda LEADERSHIP ta rawaito.
Lawan, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi, a ranar Asabar, ya bayyana rahoton da aka buga a wata jarida ta yanar gizo a matsayin “karya ce kawai”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fastoci Da Rabaran-rabaran Fiye Da 30 Ne Suka Halarci Maulidin Annabi Tare Da Musulmi A Kaduna
Shugaban Majalisar Dattawa mai wakiltar Yobe ta Arewa a Majalisar Dattawa a halin yanzu ya kara da cewa ba shi da niyyar daukaka kara a kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke zama a Damaturu a Jihar Yobe ta yanke a ranar Laraba 28 ga watan Satumba, 2022, wadda ta amince da Bashir Sheriff Machina a matsayin zababben dan takarar jam’iyyar APC na Yobe ta Arewa.
A cewar sanarwar, Lawan, ya lura cewa idan wani bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba kuma ya yanke hukuncin kalubalantarsa, to babu ruwansa da shi.
“Mun ga rahoton da Jaridar Sahara Reporters ta rawaito a yanar gizo dangane da dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023 na Sanata a Yobe ta Arewa.”
“Rahoton ya yi ikirarin cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi watsi da hukuncin da ya yanke tun farko na kin daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Damaturu a jihar Yobe ta yanke wanda ya soke takararsa a zaben.”
“Rahoton karya ce, Wata ƙirƙira ce ta ɓatanci na mai satar labaran karya da ɓarna – Sahara Reporters.”
“A karo na goma sha uku, muna so mu jaddada cewa Shugaban Majalisar Dattawa ba shi da niyyar daukaka kara a kan hukuncin da kotu ta yanke.”
“Idan wani bai gamsu ba kuma ya yanke shawarar kalubalantar hukuncin da kotu ta yanke, ba ruwansa da Shugaban Majalisar Dattawa.”
“Shugaban majalisar dattawa ya bayyana matsayinsa a fili kuma ya ci gaba Mutum ne mai maganarsa.”
Sanarwar ta kara da cewa, “Don haka muna kira ga jama’a masu hankali da suyi watsi da rahoton na jabu na Sahara Reporters ba wani abu ba face raini da ya kamace shi.”
Idan dai ba a manta ba Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a ranar 29 ga watan Satumba, Lawan ya fitar da wata sanarwa da kansa wanda ya sanya wa hannu, inda ya ce ya amince da hukuncin kuma ba zai daukaka kara kan hukuncin ba.
A wani labarin kuma, Jam’iyyar PDP Ta Bayyana Ranar Da Zata Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Ta
Jam’iyyar PDP ta bayyana shirinta na kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2023 a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba, 2022.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai, a Abuja, ranar Asabar.