Alkalin Babbar Kotun Najeriya dake Abuja mai Shari’a Binta Nyako ta bada umarnin ci gaba da tsare jagoran ta’adda na Biafra wato IPOB Nnamdi Kanu.
A ranar Litinin ne mai Shari’a Binta Nyako ta bada wannan umarni yayin zaman wata Shari’a da Kanu ya gaza bayyana gaban kotun.
Sai dai a wata takarda da Kanu ya aike wa alkalin kotun, ya ce shi sam ba a kyauta mishi ba, kuna ba za a yi mishi adalci ba muddin aka ci gaba da tsare a gidan gyara halin naka.
Kazalika ya bukaci a bashi dama da ya ga likitansa na musamman domin a cewarsa bai gamsu da likitocin da za a aike mishi ba.
Kuma tuni Nyako ta bada umarnin barin Kanu ya ga likitan nasa, amma fa ba wai za a barshi ne sakaka ba.
Kawo yanzu dai an ɗage sauraron karar jagoran Biafran har zuwa 21 ga watan Oktoba sakamakon rashin bayyanarsa a gaban kotun.
Comments 1