Wata masaniya kan harkar cutar daji wacce aka fi sani da ‘Cancer’, wato Dr Esther Ismaila, ta ce cutar dajin Nono (Mama) ana iya magance ta idan aka gano mutum na dauke da cutar da wuri.
Dr Isamaila ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi wanda Manjo Ikechukwu Eze, mukaddashin mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji a Jos.
A cewar sanarwar, Dr Esther Ismaila, ta bayyana hakan ne a waani taro da kungiyar matan ofisoshin sojoji suka shirya a Barikin runduna ta 3 ta sojin Nijeriya dake Rukuba.
Ta yi bayani ne akan gudanar da bincike akan nonon mata, wanda ta ce gudanar da bincike da wuri yana daya daga cikin matakan da ake fara gano mutum na dauke da cutar ko akasin haka.
Ta ba da shawarar cewa; ‘yan mata da shekarunsu ya kai 20, akwai bukatar su je a gwada su akalla duk bayan kwana 7 ko 10 a wata. Inda ta ce hakan ne zai sa a gano ko akwai wani kumburi, ko kuma wani ruwa ya taru bayan lokacin jinin hailarsu.
Dr Dorcas Angbazo, Kodinetan kungiyar na NAOWA a runduna ta 3, ta ce an shirya taron ne domin wayar da kan mata akan illar cutar kansar nono.