Mahukuntar gasar Tennis ta French Open sun ce za a iya korar shahararriyar yar wasan Tennis din nan lamba biyu a duniya Naomi Osaka idan har ta ci gaba da dabi’ar kin hira da yan jaridu.
Yar wasan yar kasar Japan ta ce ba za ta sake cewa uffan ma yan jarida ba a yayin gasar da ake kira da Grand Slam, domin ci gaba da kare lafiyarta da ta shafi ƙwaƙwalwa.
A yau Lahadi be aka ci tarar Osaka dala dubu sha biyar, bayan da ta gaza zantawa da manema labarai a dukan kawo wuka da ta yi wa yar kasar Romaniyar nan Patricia Maria a yau Lahadin.
Wasan nasu ya karkare ne sa ci 6-4 7-6 (7-4)
Cikin wata takardar hadin gwiwa da mashirya gasar suka fitar sun ce muddin Matashiyar ta kuskura ta sake aikata haka, to za a sake cin tararta, kuma za ta fuskanci hukuncin dakatarwa.