Sashin dake kula da harkokin man fetur ta Kasa watau (DPR), sun alkarwatama Mutanen Najeriya za su wadata da man fetur a lokacin bikin babbar Sallah.Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Mista Paul Osu, shugaban hulda da jama’a na cibiyar, ya bada tabbacin haka a wani bayani daya gabatar a ranar Juma’a a Legas.
Gwamnatin tarayya dai ta sanya Talata 20 ga watan July da kuma Laraba 21 ga watan July na wannan shekarar a matsayin ranakun shagulgulan Sallah.
KARANTA:- FG ta sanar da 20 da 21, July a matsayin ranakun hutun Sallah
Osun yace, da akwai man fetur sosai, ya kuma yi kira ga Yan kasuwa da kada su rinka boye man fetur da nufin kuntatawa al’umma.
Yace sashen DPR zaibi diddiqin zirga-zirgan wajan tabbatar da an samar da wadatacce kuma ingantattaccen man fetur abisa yadda dokar sashen ta tsara.
Osun, ya kuma shawarci jama’a dasu Kai rahotan duk wanda suka ga yana boye man fetur ko yana misantashi ga hukumar DPR mafi kusa dashi a fadin kasar nan.
Ya kara jawo hankalin mutane dasu cigaba da bin doka kamar yadda sashen ya tsara na yin dakon man fetur ko amfani da man fetur.
Osun ya cigaba da cewa sashen na iya kokarin sa wajan samar da hanyoyi daban-daban wanda za a samar ma masu jari da sauran Yan kasuwanni dama da hanyoyi daban-daban.
A wani labarin
Ganduje ba mugu bane, cewar shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ba mugu bane.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka a wani gayyata na musamman da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero yayi masa a ranar Alhamis.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yabawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan irin ayyukan da ya kaddamar, yace cigaba da ayyukan da tsohon gwamna yayi ya nuna irin adalci na mulkin Ganduje.
Ya kuma yi kira da yin koyi da irin wannan hali na gwamna Ganduje, Shugaba Muhammadu Buhari yace yana jindadi yaga gwamna ya fara aiki kuma ya kammala shi.
Buhari yace yaji matukar dadi ganin yadda Ganduje ya kammala aikin da tsohon gwamnan ya bari.
Wannan ya nuna cewar Ganduje ba mugu bane ko kuma azzalumi.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nuna farin cikinsa gami da mutanen Kano kan irin ayyukan da shugaban Kasa ya gudanar a Jahar.
Gwamnan yace irin ayyukan sune kamar kaddamar da layin dogo da zai tashi daga Kano zuwa Kaduna wanda Shugaban kasa ya kaddamar a ranar 15 ga watan July.