Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi barazanar cewa zai yi yaki domin ganin ya gama da duk wanda yake aiki da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, kamar yadda jaridar DAILYPOST ta rawaito.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Secondus dai na hannun damar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne.
Wike ya yi wannan barazanar ne a ranar Asabar din nan a wajen bikin kaddamar da gina titunan cikin garin Omagwa da ke karamar hukumar Ikwerre a jihar Ribas.
PDP Na Tafiyar Hawainiya A Kokarin Sasanta Atiku Da Wike, Tsohon Shugaba
Gwamnan ya ci gaba da cewa zai “gama” da duk wanda ya kafa tantinsa da “makiya jihar”.
Ya ce, “Idan wani ya yaki tsarinmu, za mu yaki mutumin.
“Bari in gaya muku abin da ba ku fahimta ba a siyasa. A duk lokacin da kuka ce kuna aiki tare da mu kuma gobe kuka koma ga makiyinmu, za mu dauki dukkan karfin da muke da shi, har ma za mu bar makiyinmu mu gama da ku tukuna.
“Don haka dukkan ku da za ku koma Abuja domin yin taro da makiyanmu a jihar, zan karasa ku zuwa karshe.
“Mun tsige Shugaban Jam’iyyar na Kasa wanda baya aiki mai kyau. Dukkansu suna nan, duk mun amince, yanzu za su je Abuja su yi taro da mutumin da muka cire, a tunanin ku za ku yi amfani da wannan wajen yakar mu, za mu murkushe su”.
Wike ya jagoranci yakin neman tsige Uche Secondus a matsayin shugaban PDP na kasa a shekarar 2021 da ta gabata.