Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi, ya bayyana Bola Ahmed Tinubu, na jam’iyyar APC a matsayin mafita ga kalubalen Najeriya.
Ya kuma bayyana Tinubu a matsayin wanda ya hada kai da ayyukansa suka yi tasiri wajen wada Najeriya wuri guda.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alli Ibraheem, babban sakataren yada labaransa, Oba Akanbi ya bayyana cewa a matsayinsa na dan Najeriya, Tinubu ya mayar da jihar Legas ta zama abin koyi ga sauran Jihohin kasar.
A cewarsa, “Tinubu dan Najeriya ne da aka wulakanta shi. Irin nasarorin da ya samu wajen mayar da jihar Legas tamkar wani katafaren ido, abin yabo ne matuka, Amanar Najeriya a hannunsa yakamata ya zauna, Za ku ga abin mamaki idan aka bashi dama”.
Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Kafa Dokar ta ɓaci a Karu, Jahar Nasarawa
Yayin da yake rokon wadanda suka yi Allah wadai da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Oluwo ya kara da cewa mulki ba shi da alaka da shekaru.
“Yawancin wadanda ke kalubalantar Tinubu na da al’amuran kashin kansu. Mutane da yawa suna cewa yana da girman kai domin yana faɗin gaskiya.
“Mutane suna iya tunanin shi mai girman kai ne domin yana faɗin gaskiya. Duk wanda ya fadi gaskiya an shar’anta shi da girman kai. Mutane suna cewa ni ma mai girman kai ne. Domin ina ƙaunar gaskiya kuma ina fadin ta.
“A ba shi Najeriya ya yi mulki ya rike, Zai yi abun al’ajabi kafin ka wani lokaci,” in ji shi.
A wani labarin kuma na daban.
Gwamna Abiodun ya taya Pantami murnar samun Lambar yabo daga Cibiyar CIISEC
Gwamnan Jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya taya Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, murnar samun lambar yabo ta Cibiyar Adana sahihan bayanai kan tsaro (CIISEC).
Gwamnan, wanda ya ce ya ji dadin wannan labari, ya ce wani abin alfahari ne da ya cancanci a taya shi murna.
Da yake magana ta wata sanarwa ta hannun Babban Sakataren yada labaran sa, Kunle Somorin, Gwamna Abiodun ya ce Pantami bawai kansa kaɗai zaiyi alfahari ba, har da kasa da baki ɗayan baƙar fata.
“Wannan abin tarihi ne, wata nasara ce, kuma ban yi mamakin abokina da ɗan’uwana ya sami karramawa ba,” in ji Gwamna Abiodun.
An shigar da Pantami a matsayin ɗan Afirka na farko kuma tilo a cikin CIISec a cikin mutane 89 da suka lambar yabon.
Gwamnan ya ce ba abin mamaki ba ne, idan aka yi la’akari da irin kwazo da jajircewa da ministan ke yi a aikinsa.
“Yana da sha’awar duk abin da yake yi; hazikin mutum ne kuma ba wanda zai ɗauki aiki don sonsa kawai ba.
“A yau, a cikin sararin samaniyar yanar gizo na duniya, Pantami babban dan wasa ne. Wannan wani ci gaba ne da ake maraba da shi domin zai taimaka wajen haɓaka sashen IT ɗin mu.
“Saboda haka, dole ne mu kuma taya CIISEC murnar samun damar gane wadanda suka cancanci a karrama,” in ji shi.
Gwamna Abiodun ya bukaci ministan da ya kara kaimi, kada ya hakura, yana mai cewa hakan na nuni da samun nasarorin da yake samu.