David Lyon ya lashe tikitin jam’iyyar APC na tsayawa takarar gwamnan jihar Bayelsa a zaben fidda gwanin da ya gudana. Ya samu kuri’a 42,138, a yayin da Diseye Nsirim ta biyo shi a baya a matsayin na biyu da kuri’a 1,533.
Sauran da suka tsayawa takarar sun hada da; Heineken yLokpobiri, wanda ya samu kuri’a 571, sai Preye Aganaba, da ya samu kuri’a 354 sai kuma Amgbare da ya samu kuri’a 633 sai Farfesa Maureen Etebu da ya samu kuri’a 564.
Sanata Dangana Emmanuel, shi ne ya bayyana hakan a garin Yenaguwa. An gudanar da zaben kato bayan kato ne kamar yadda kwamitin masu ruwa da tsaki suka bukaci hakan.
Gwamna Mai-Mala Buni na Yobe shi ne ya jagoranci kawo sakamakon zaben.