A safiyar yau ne dai kotun shari’ar zabe na kasa za ta fara saurarar shari’ar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC game da zaben shugaban kasa na 2019 da ya gabata.
Tuni dai kotun ta mikawa kowannen su takardar sanarwar fara zaman saurarar shari’ar ta yau.
Zaman Wanda ke gudana a halin yanzu Wanda mai shari’a Zainab Bulkachuwa, ke jagoranta.
Mahalarta zaman na yau sun hada da Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa na PDP Mista Peter Obi, da lauyoyin su.
Ana sa rai kotun za ta hadu da dukkan bangarorin biyu a yau don jin hujjoji da bayanan su.
Baya ga karar da dan takatar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku ya shigar a gaban kotu yana kalubalantar zaben Muhammadu Buhari, akwai ‘yan takarar jam’iyyar HDP Cif Ambrose Owuru da kuma dan takarar jam’iyyar PDM Pasto Aminchi Habu da suka shigar da kara.
Ana shi bangaren Atiku Abubakar yayi alwashin bankado sakamakon zaben shugaban kasar a gaban kotun shari’a.