Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya murna ga Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa-NUJ, akan sakamakon daya fito bayan taron shuwagabanni da akayi kashi na bakwai, wanda aka sake zaɓar Chris Isiguzo a karo na biyu a matsayin shugaban ƙungiyar na Ƙasa.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar “bayar da ƴanci ga ƴan jarida abune da baza’a iya rage shi a tsarin Dimokuraɗiyyar dake son kawo cigaba, a saboda haka dole ayi amfani dashi yanda ya kamata.
Ta la’akari da irin gudummawar kafafen yaɗa labaru ke bayarwa wajen wayar wa mutane kai akan al’amurran kowacce al’umma, Shugaban Ƙasa ya tunatar da Shuwagabancin NUJ cewa ƙasar zata cigaba da sa ido akan aikin jarida mai cike da ƙa’idoji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ma’aikatar Lafiya Ta Kafa Tsirrai Dan Samar Da iska Mai Kyau A Cikin Jihohi 36 –NEC
Shugaban Buhari ya yi kira ga kafafen yaɗa labaru dasu maida hankali wajen haɗin kai a cikin ƙungiyar, tare da cigaba da tattaunawa domin sasanta duk wata matsala da zata taso domin cigaban ƙungiyar.
Shugaba Buhari ya baiwa sabbin shuwagabannin ƙungiyar tabbacin cewa, gwamnatin sa zata cigaba da kare dukkanin haƙƙoƙin kafafen watsa labarai kamar yadda yake cikin kundin tsarin Mulkin Najeriya