Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya soki shugabannin ƙasar nan masu ci da waɗanda su ka gabata a kan kasa cika alkawuran da su ka ɗaukar wa ƴan ƙasa.
Tinubu ya ce zai magance matsalolin da suka kasa magancewa idan aka zabe shi a amatsayin shugaban kasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobara ta ƙone Wani Bene a Ilori
Jaridar Premium Times ta ruwaito Tinubu na yi wa wasu daruruwan matasa jawabi ne da suka taru domin nuna goyon bayansu a gare shi.
Ya ce, “Muna sane da fushinku. Ban ga laifinku ba, alkawuran da a ka sha yi muku a baya sun kasa biyan bukatunku, tun daga lokacin da kuke makarantar firamare. Ba za mu ci gaba da halayya irin ta da ba.”
A cikin jawabin, wanda aka nada a bidiyo, Tinubu bai bambanta tsakanin gwamnati mai-ci ta Muhammadu Buhari ba da ta shugabannin da ya gada.
Duka Tinubu da Buhari ƴaƴan jam’iyya ɗaya ne, kuma Tinubu ya nemi goyon bayan Shugaba Buhari gabanin ayyana burinsa na tsayawa takara.