Wani magidanci mai suna Sunday Enejo, ya buƙaci wata kotun kostomare dake a Jikwoyi a birnin tarayya Abuja, da kada ta amince da roƙon da matar sa tayi na raba auren su.
Magidanci ya nemi kotun da ta sanya matar sa da tayi rantsuwa da abin bautar su mai suna Aniku, cewa bata taɓa cin amanar sa ba da wani namiji a waje ba. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: An ɗaure Makiyaya 2 shekara 5 kowannensu bisa laifin satar shanu 14
Matar tasa mai suna Rose wacce take ƴar kasuwa ce a cikin ƙarar da ta shigar tana neman a raba auren su, ta bayyana cewa Enejo mutum ne mai rigima kuma yana dukanta kusan koda yaushe.
Sai dai, Enejo ya ƙi yarda ya amince ya saki Rose har sai ta rantse da Aniku, cewa bata baɗala da wasu mazan a waje.
“Ba zan saki mata taba har sai ta biyo ni mun je ƙauye ta rantse a gaban Aniku cewa bata baɗala da wasu mazan a waje.” Ya gayawa kotu.
Alƙalin kotun, Labaran Gusau, ya ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 4 ga watan Afrilun 2023 domin cigaba da sauraron ƙarar.