Dalilan da yasa gwamnatin rikon kwarya ba za ta faru a karkashin ikon Buhari – Lalong
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ce gwamnatin wucin gadi da za ta dakatar da bikin rantsar da Bola Tinubu ba za ta yi aiki karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.
Lalong ya bayyana haka ne a ranar Alhamis bayan ganawa da Buhari a Aso Rock.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wani Gwamna Ya Kori Dukkanin Hadiman Sa Daga Aiki
Kalaman nasa ya zo ne sa’o’i 24 bayan jam’iyyar All Progressives Congress, APC da Peoples Democratic Party, PDP, sun kalubalanci hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, da ta cafke masu yunkurin kafa gwamnatin wucin gadi ta kasa.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu a gaban Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party da Peter Obi na jam’iyyar Labour.
Sai dai, bayan sanarwar INEC, Atiku da Obi sun yi watsi da sakamakon da ake zargin an tafka magudi a zaben.
Tare da fadace-fadacen shari’a, an yi ta maganar kafa gwamnatin wucin gadi.
Lalong ya ce: “Ba a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari ba, wanda a duk lokacin da ya ke cewa ‘Na yi imani da dimokradiyya. Na yi imani cewa bayan aiki na, ina so in je in huta.’
“Don haka wadanda har yanzu suke magana a kai (gwamnatin wucin gadi), zan ce mafarki ne kawai suke yi. Da yardar Allah Buhari zai kawo wanda zai gaje shi kuma wanda zai gaje shi ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A wani labarin kuma:“Zan Saki Matata Amma Sai Ta Rantse Bata Taba Badala Da Wasu Mazan Ba”, Magidanci Ga Kotu
Wata Kotun Majistare da ke Gwagwalada, babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wasu barayin biyu Buba Bello da Abubakar Umar hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari kowannen su da aikin wahala bisa samunsa da laifin satar shanu 14 da kudinsu ya kai Naira miliyan 2.5.
‘Yan sandan sun gurfanar da Bello mai shekaru 30 da Umar mai shekaru 26 da laifin hada baki, tsoratarwa, zamba, sata da kuma karbar kudi.