Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta jaddada kudirinta na cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar baki daya
Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar da aka turo ne ya bayyana haka ne a lokacin da yake gudanar da taron manema labarai jim kadan bayan ya fara aiki a helikwatar ‘yan sandan jiha nan da ke Birnin Kebbi a yau Talata.
Kwamishinan Magaji Ahmed Kontagora wanda ya fito daga karamar hukumar Kontagora ta jihar Neja, ya ce jagorancin sa szai yi aiki tare da aiwatar da wasu dabarun siri na yaki da miyagun laifuka a fadin jihar Kebbi.
Ya kara da cewa rundunar yan sanda ba za ta lamunci aikata laifuka ba, don haka ya gargadi duk masu aikata laifuka a jihar da masu su tunanin aikatawa da su janye kudirin nasu domin jihar ta zauna lafiya.
Zaben Kenya: Fiye da Mutum miliyan 6 ne suka kada kuri’a kawo yanzu—- Hukumomi
Kazalika Kwamishinan ya ce za su hada kai da sauran hukumomin tsaro, malaman addini , da ma shugabanin addinai domin yakar matsalar tsaro a fadin jiha baki daya.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi karkashin jagorancinsa za ta yi wa kowa adalci ba tare da la’akari da babbancin kabila, ko matsayi ba cikin al’umma ba.
Daga nan sai ya bukaci jama’a da su rinka baiwa rundunar bayanai masu amfani domin dakile laifuka da samar da tsaro a jihar.
CP Magaji Ahmed, ya gadi CP. Musa Baba, wanda ya yi ritaya daga aikin rundunar ‘yan sandan Najeriya.