Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu da mataimakin dan takarar shugaban kasa , gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, za su jagoranci zanga-zangar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar zuwa hedikwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) dake Abuja.
Zanga-zangar ta biyo bayan zaben shugaban kasa ne da kuma ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da alkalan zaben suka sanar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Afirka Ta Kudu Zai Yiwa Majalisar Ministocin sa Garambawul A Ranar Litinin
Idan ba a manta ba a karshen tattara sakamakon zabe a makon jiya, INEC ta bayyana tsohon gwamnan jihar Legas a matsayin wanda ya lashe zaben da jimillar kuri’u 8,794,726 sai dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar wanda ya samu kuri’u 6,984,520 da kuma Peter Obi mai kuri’u 6,101,533, bi da bi.
Tuni dai ‘yan takarar jam’iyyar PDP da LP suka yi watsi da sakamakon zaben bisa hujjar cewa an yi amfani da alkaluman dan takarar jam’iyya mai mulki.
Suna zargin hukumar zaben da rashin gudanar da ingantaccen zabe, kuma dukkansu sun nuna aniyarsu ta kalubalantar sakamakon a gaban kotu.
Yanzu haka dai babbar jam’iyyar adawa ta yanke shawarar cewa ita ma a zahiri ta bayyana rashin amincewarta da sakamakon zaben inda ta yi tattaki zuwa hedikwatar INEC da ke Maitama a Abuja.
Tuni dai jam’iyyar ta fara tattara manyan masu ruwa da tsaki domin gudanar da tattakin da aka ce za ta tashi daga sakatariyar ta ta Legacy House da ke Maitama da karfe 10 na safe.
Wasikar gayyata da daraktan gudanarwa na kungiyar dan takarar shugaban kasa ta PDP ya fitar, ya lissafa shugabannin jam’iyyar da ake sa ran shigar su zanga-zangar sun hada da Ayu, Okowa; Shugaban jam’iyyar PDP PCO kuma gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, da babban darakta na kungiyar kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.
Sauran sun hada da Gwamna Duoye Diri (Bayelsa), Godwin Obaseki (Edo), Ahmadu Fintiri (Adamawa), Bala Mohammed (Bauchi), Darius Ishaku (Taraba), da Ademola Adeleke (Osun).
Haka kuma an gayyato tsaffin shugabannin majalisar dattawa, Sanata David Mark da Dakta Abubakar Bukola Saraki, dukkanin mambobin kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BOT), mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NEC), ‘yan jam’iyyar PDP a majalisar dokoki ta kasa, mambobinta da Kwamitin Ayyuka na kasa (NWC) da dai sauransu.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa kuma daraktan hulda da jama’a, Sanata Dino Melaye, ya tabbatarwa da jaridar Nigerian Tribune zanga-zangar.
Da aka matsa masa don ba da makasudin atisayen, ya ce: “Zanga-zanga ce. Idan kun zo gobe, za ku ji abin da za mu gaya musu.”
A wani labarin kuma, Idan Kuka Zabe Ni, Zan Biya Kowane Matashi Naira 30k Duk Wata — Dan Takarar Gwamnan SDP
Dan takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party a jihar Delta, Cif Kenneth Gbagi, ya yi alkawarin gyara masakun Asaba idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar a zaben da za a yi ranar Asabar, Punch ta rawaito.
Gbagi ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake jawabi a wani gangamin da ya samu halartar fastoci daga coci-coci daban-daban da kungiyoyin mata a cikin babban birnin Asaba ranar Asabar.