Daruruwan mata da suka hadar da iyayan daliban da a kayi garkuwa dasu a Makarantar Bethel Baptist, da sanyin safiyar yau Litinin. Sun toshe babban hanyar Kachia a Maraban Rido, inda su keyin zanga-zanga, domin nuna bacin ran su a kan sace yaran na su.
Hakan ya biyo bayan sace daliban makarantar Bethel Baptist da Yan bindiga su kayi a safiyar yau Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalissar Kano ta dakatar da Muhuyi Magaji
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, damu salin karfe uku na yammacin nan ne dai, Matan suka fito da katakai da kuma itace, inda su ke hana mutane bin hanyar.
Kazalika daga bisani Jami’an soji sun iso inda lamarin ke afkuwar da misalin karfe 3 da Minti 5, inda su kayi kokarin bude hanyar.
Akwai Karin bayani………….