Majalissar dokokin jihar Kano ta dakatar da Shugaban hukumar amsan koken al’uma da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Muhuyi Magaji Rimin Gado, har na tsawon wata guda.
An dakatar da Magaji ne bisa kin amince wa da bindiddigi da babban Ankanta na jihar ya bukaci a yi a kan shi.
Hakan ya biyo bayan takaddar korafin da ofishin Babban Akanta na jihar ya turawa majalissar dokokin jihar.
Wasikar ta yi nuni da cewa, an bai wa Shugaban mukamin hukumar ne, a mataki na 4, Wanda hakan ya sabawa dokar jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar soji ta sake samun nasar
Shugaban majalissar jihar Alhaji Labaran Madari, ya umarci majalissar da ta mika bayanan wannan lamarin ga kwamitin dake kula da binciken cin-hanci da rashawa da kuma daukar mataki.
Kazalika majalissar dokokin ta bukaci Kwamitin da ta mika cikakken rahoton ta, ga majalissar nan da mako biyu masu zuwa.