Jami’an tsaro a jihar Katsina sun kama shugaban kungiyar Northern Group Congress (CNG), wanda ya jagoranci yin zanga-zangar lumana gane sa rashin tsaro da ake fuskanta a jihar Katsina.
Wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar sun shaidawa wakilinmu cewa jami’an tsaro sun kama Nastura Ashir Sharif, kuma sun tafi da shi babban birnin tarayya Abuja.
Shaidun suka ce an kama shi ne jim kadan bayan da kungiyar ta shirya-zanga zangar lumana saboda yawan kashe-kashen jama’a da ‘yan bindiga ke yi a jihar Katsina.
A yayin da muka yi kokarin jin ta bakin kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isa yaci tura.
Har yanzu dai babu wani rahoto daga ɓangaren jami’an tsaron game da kama shugaban kungiyar.