Akalla mutum guda daya likita ne ya rasu sakamakon zazzabin cutar lassa yayin da wasu biyu ke kwance a asibiti a Makurdi babban birnin jihar Benue.
Marigayin, likita mai suna Samuel Nyityo, wanda ma’aikaci ne a hukumar lafiya ta duniya, (WHO) a jihar Benue, an ce ya yi rashin lafiya kuma an garzaya da shi asibitin kwararru na Irrua da ke jihar Edo inda daga baya ya rasu.
A cewar wani ma’aikacin asibitin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa manema labarai cewa mutane uku ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar.
Da aka tuntubi Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jama’a na Jihar Binuwai, Joseph Ngbea ya tabbatar da cewa akwai zazzabin lassa a jihar amma ya musanta ikirarin cewa mutane uku ne suka mutu sakamakon cutar.
Dakta Ngbea ya ce mutum daya ne kawai ya mutu sannan kuma wani da ya kamu da cutar yana samun kulawa kuma yana cikin kwanciyar hankali a asibiti.
Yayin da ya ke bayyana cewa gwamnatin jihar na iya bakin kokarinta wajen ganin an shawo kan cutar, kwamishinan ya bayyana cewa, kafin a gano cutar ta zazzabin lassa, gwamnan jihar Samuel Ortom, ta hannun ma’aikatar ya fitar da kudi domin ganin an dauke shi.
Kwamishinan wanda ya kuma tabbatar da cewa Marigayi Dokta Nyityo ya yi aiki da hukumar ta WHO ya ce Gwamna Ortom ya je ya dauki nauyin biyan kudin amma sun ce a’a kungiyar ta sake siyan magungunan da ya kai Naira 600,000 domin baiwa duk wanda ya kamu da cutar.
Dakta Ngbea wanda ya shawarci jama’a da su daina cin bera ya bayyana cewa WHO ta bukaci jama’a da su tabbatar da cewa duk wanda ya kamu da cutar a kai shi asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benue BSUTH cikin mintuna 20.
Ya ce ma’aikatar za ta shirya wani taron karawa juna sani kan cutar zazzabin lassa a jihar domin kara wayar da kan jama’a kan dalilin da ya sa ba za su ajiye duk wani abu da zai kawo beraye a gidajensu ba.
Comments 1