Shugaban sashen tsare-tsaren kasuwanci na OTrike, wani kamfanin zirga-zirga ta hanyar sadarwa, Collins Nzeribe ya ce kamfanin na su ya yi nasarar hada kan mutanen Jos ta hanyar ayyukansu na zirga-zirga.
Nzeribe ya ce kamfanin na su yana ci gaba da gamsar da al’ummar yankin ta hanyar daukar su a Keke Napep ga duk inda za su a yayin zirga-zirgar su. Ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Nijeriya a ranar Litinin cewa; Fasinjoji yanzu suna samun damar zuwa duk inda za su je a garin Jos, hatta har wurin da ake ganin yana da hatsari zuwa wurin, sakamakon rikice-rikicen addini da ya auku a garin.
Ya ce amma zuwansu da wannan sabon tsari na zirga-zirga ya taimaka matuka gaya wajen hada kan al’ummar garin wadanda suke da bambance-bambance a addini. Ya ce musamman yadda su masu daukar fasinjoji ba zabar wanda za su dauka suke yi ba.
Ya tabbatar da cewa tsarin na su ya kawar da tsoro da firgicin da yake akwai a tsakanin al’umma wanda hakan ya takaita zirga-zirga zuwa wadansu yankunan.