Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kai ziyara Monguno inda ya shafe kwana biyu a garin.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai Isa Gusau ya aike wa BBC a ranar Laraba.
Yayin ziyarar, gwamnan ya iza harsashin ginin gidaje 1,000 domin ‘yan gudun hijira da suka yada zango a makarantu.
Gwamnan ya kuma iza harsashin ginin makarantar Islamiyya wadda za ta samar wa da mutum 10,000 da ke da ilimin addinin Musulunci damar samun difloma a ilimin zamani.
Akwai ‘yan gudun hijra 89,000 da ke zaune a Monguno wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.
Kwamishinan sake gina Borno Injiniya Mustapha Gubio ya ce an iza harsashin gina rukunin gidajen domin samar wa ‘yan gudun hijrar wajen zama.
Ya ce hakan zai bai wa makarantun da ‘yan gudun hijrar suka mamaye damar komawa bakin aiki.