Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai keta hazo zuwa Kasar Birtaniya don duba Lafiyar shi.
Hakan ya fito ne ta bakin Babban Mai Baiwa Shugaban Kasar Shawara Kan yada labarai Femi Adesina.
To sai dai gabannin tashin jirgin Shugaban Kasar, zai gana da manyan Hafsoshin tsaron kasar da sanyi safiya.
Ana Kuma sa ran Shugaba Buharin zai komo gida Najeriya ne mako na biyu cikin watan Afirelu.