Gwamnatin jihar Borno ta sanar da rasuwar Sarkin Biu, Mai-Umar Mustafa-Aliyu, wanda ya rasu da sanyin safiyar Talata ɗin nan.
Kwamishinan harkokin cikin gida, yaɗa labarai da al’adu Alhaji Babakura Abba-Jato ne ya sanar da rasuwar a cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.
Abba-Jatu yace ” Inna lillahi wa inna ilahi rajiun, Allah ya karɓi ran mai martaba Sarkin Biu, Mai-Umar Mustafa-Aliyu”.
“An naɗa mai martaba Sarkin Biu kan mulki a shekarar 1989, ya kuma rasu da sanyin safiyar nan yana da shekaru 80 a duniya. Za a birne shi da misalin ƙarfe 2 na yamma, kamar yadda masarautar ta bayyana, Allah ya jiƙansa, amin”.