Sama da masallatai 1500 ne Saudiyya za ta bude a Makkah a ranar Lahadi 21 ga watan Yuni domin ba wa masallata izinin yin ibada a cikinsu, kuma an yi feshin magani a masallatan.
Wannan matakin na zuwa ne kafin lokacin aikin Hajji da ke zuwa a karshen matan Yuli, kuma zuwa yanzu mahukuntan kasar ba su kai ga yanke hukuncin ko za a yi aikin Hajji bana ko akasin haka.
Garin Makkah shi ne matattarar Alhazzai amma wani rahoto da kamfanin dillancin labaru na AFP ya ruwaito ya cewa duk da kwararan matakan kariyar cutar da mahukantan kasar ke dauka musamman a Birnin Makkah ana ci gaba da samun yawaitar yaduwar cutar a kasar.
Gwamnatin kasar ta bude masallatan da ke wajen Birnin Makkah ne tun a watan Mayu inda ake yin sallah a bisa ka’idar ba da tazara.
A kasar ta Saudiyya sama da mutum 150,000 ne suka kamu da cutar COVID-19 yayin da fiye da mutum 1200 suka rasu a sakamakon cutar.