Ɗaya daga cikin waɗanda hatsarin jirgin saman ranar Juma’a a Legas ya ritsa da shi ya rasu, bayan awanni da kai shi asibiti.
Tun bayan faɗuwar jirgin mai saukar ungulu a yakin Ikeja matuƙansa biyu suka rasu yayin da aka garzaya da mutum na uku da ke cikin jirgin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LASUTH).
Shaidu sun ce da zuwa da shi an wuce da shi ɓangaren tiyata ne saboda yana cikin tsananin mawuyacin hali.
Rahotanni sun ce daga baya shi ma ya cika duk da dai hukumomi ba su kai ga sanarwa ba.
“Abin takaici yanzu mutum uku ke nan suka rasu, da suka haɗa a matuƙin jirgin, Chika Prudence Ernest da injiniyan jirgin Clement Ndiok”, inji majiyarmu.
Tuni dai hukumar binciken haɗurran Jiragen Sama (AIB) ta ɗauki akwatin naɗar bayanan jirgin domin fara binciken musabbabin hatsarin na ranar Juma’a.
Gabanin azahar ne jirgin mai ɗauke da mutum uku ya faɗo a cikin wasu gidaje.
Hukumomin agaji da masu kashe wuta a jihar Legas, tun da farko sun tabbatar da faruwar lamarin da kuma waɗanda abin ya ritsa da su.