Hukumar ƴan sanda jihar Anambra ta bayyana cewa ta cafke wata mata mai suna Mrs Akunna Roseline Udom, mai shekara 35 a duniya bisa zargin damfara da zamba cikin aminci.
Kakakin hukumar ƴan sandan, DSP Ikenga Tochukwu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairun 2023. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: An Sake Samun Girgizar Kasa A Turkiyya
Kakakin yace mata tana cikin wata tawagar wasu ɓata gari da suka ƙware wajen aikin damfara da zamba cikin aminci.
A cewar sa tana yaudarar ƴanmata da yi musu alƙawarin ƙarya na cewa zata sanya ɗan’uwanta dake zaune ƙasar waje ya aure su.
Kakakin yace matar ta damfari sama da ƴanmata biyar kuɗaɗen da suka wuce naira miliyan tara (N9m).
“Roseline tana ɗaya daga cikin tawagar wasu ɓata gari waɗanda suka ƙware wajen damfarar mutanen da basu ji ba basu gani ba.”
“Ta amsa cewa waɗanda take damfarar ƴanmata waɗanda ke aiki a bankuna, aikin gwamnati inda take basu tabbacin cewa ɗan’uwanta wanda yake zaune ƙasar waje yana neman matar aure.” A cewar sanarwar
Rabon Ajali: Matashi Ya Nutse a Rijiya Wajen Ciro Bokiti
A wani labarin na daban kuma wani matashi ya nutse a cikin rijiya wajen ciro bokiti
Wani matashi mai shekara 27 a duniya ya nutse a rijiya yayin ƙokarin ciro bokitin da ya faɗa cikin rijiya.
Lamarin dai ya auku ne a ƙauyen Alaja cikin ƙaramar hukumar Akinyele ta jihar Oyo.
A cewar majiyar, mamacin yaron mota ne sannan da shi da ogan sa direban babbar mota suna kan hanyar su ta zuwa wani waje ne a jihar