Kotu ta tasa Ƙeyar wani Ɗan kasuwa Gidan Gyaran Hali wata 17 kan Laifin Damfarar Kwastoma
A ranar Juma’a ne wata kotu mai daraja ta ɗaya da ke Lugbe Abuja ta yanke wa wani dan kasuwa Isa’ic Onah mai shekaru 39 hukuncin daurin watanni 17 a gidan yari bisa samunsa da laifin damfarar Abokin cinikayyar sa Naira miliyan 1.
An yanke wa Onah mazaunin Tekan ta Masaka Jihar Nasarawa hukunci bisa wasu laifuka biyu da suka haɗa da zamba da cin amana bayan an yadda da shi.
Sai dai alkalin kotun yankin Aliyu Kagarko ya baiwa mai laifin zaɓin biyan tarar Naira 60,000 yayin da ya kuma umarce shi da ya biya Naira 1,150,000 a matsayin kuɗaɗen da wanda ya kai karar a kan su.
Ya kuma gargaɗi wanda aka yankewa hukuncin da ya kasance mai kyawawan halaye a yayin mu’amalar shi da mutane.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa tun da farko Onah ya amsa laifinsa inda ya roƙi kotun da ta yi masa sassauci.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Dumi-Dumi: An Yanke Wa Bishop Hukuncin Daurin Rai da Rai Bisa Wasu Tuhume-Tuhume
Dan sanda mai shigar da kara Mista Olisaemeka Okeke ya shaida wa kotun cewa a ranar 15 ga watan Janairu mai shigar da kara Mista Analife Onyekachi na Wuye Abuja ya kai karar ofishin ‘yan sanda na Durumi.
Okeke ya ce wanda ya shigar da karar ya yi ikirarin cewa a ranar 5 ga watan Janairu mai laifin ya yaudare shi tare da karbar Naira 1,150,000 a wurinsa da sunan dillalin mota.
Ya ce wanda ake tuhuma da laifin ya yaudari wanda ya kai karar cewa zai taimaka masa wajen siyan mota kirar Honda Accord amma ya gudu da kuɗin zuwa wani wuri da ba a sani ba, sannan ya mayar da kudin zuwa amfanin kansa.
Mai gabatar da ƙara ya ci gaba da cewa a yayin binciken ‘yan sanda sun ce mai laifin ya yi furuci da cewa duk kokarin da aka yi na kwato kuɗaɗen ya ci tura.
Okeke ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 312 da 322 na kundin laifuffuka.