- Rundunar ‘yan sandan Yobe ta sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin hada baki da kuma sata
- An kama wadanda ake zargin dauke da jarkoki da bututun jan mai suna tsaka da kokarin yashe man
- Masu laifin zasu fuskanci fushin doka da zarar an Kammala bincike
Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin hada baki da kuma satar man dizal na taransifoma.
Sanarwar ta fito ne a cikin wani rahoton halin da ake ciki daga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar, Dungus Abdulkarim, wanda aka rabawa manema labarai a Damaturu ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Ribas ta Kada Wata Kuri’a Kan Gwamna Fubara
Kakakin ‘yan sandan ya ci gaba da cewa, “Ina godiya da sanar da ku cewa a ranar 24/01/2024 da misalin karfe 02:00 na safe, tawagar ‘yan sanda tare da ‘yan banga karkashin jagorancin P&G ASP Lukman Usman a lokacin da suke sintiri, suka kama wani Bala Sa’idu na karamar hukumar Numan, jihar Adamawa, da Wani Suraja Adamu na karamar hukumar Gamawa dake jihar Bauchi.”
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin dauke da jarkoki takwas na man dizal da bututun jan mai a hanyar Jakusko/Golo.
Kakakin ya kara da cewa a yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma ana gudanar da bincike a kan lamarin domin sanin matakin da suka dauka.
Dungus Abdulkarim ya bada tabbacin cewa za a sanar da sauran al’umma gaba daya.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: An Yanke Wa Bishop Hukuncin Daurin Rai da Rai Bisa Wasu Tuhume-Tuhume
Wata Kotun Laifukan Jima’i da Laifukan Cikin Gida da ke Ikeja ta yanke wa wani Bishop a Legas, Oluwafeyiropo Daniels, hukuncin daurin rai da rai
Hakan ya biyo bayan laifin yin lalata da mataimakiyar sa ‘yar shekara 23
Alkalin kotun ya ba da umarnin cewa malamin ya ci gaba da zama a gidan kurkukun Kirikiri
Wata Kotun Laifukan Jima’i da Laifukan Cikin Gida da ke Ikeja ta yanke wa wani Bishop a Legas, Oluwafeyiropo Daniels, hukuncin daurin rai da rai kan laifin yi wa mataimakiyar sa ‘yar shekara 23 fyade (wanda aka sakaya sunanta).
Mai shari’a Rahman Oshodi ya kuma yankewa Daniels, Bishop na cocin I Reign Christian Ministry dake Legas, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa samunsa da laifin yin lalata da wata mambar cocin ‘yar shekara 19.