Wata da ba’a san ko wacce ba ta mutu, bayan wani harsashin ya kwace ya same ta, a wurin Gangamin masu rajin kafa kasar Yarbawa da ke gudana a Filin taro na Ojota, da ke jihar Legas a yau Asabar.
Zanga zangar dai an fara ta ne da wakoki, da iface-iface, inda daga bisa ni abun ya girma-ma, har sai da jami’an tsaro suka fara harbi sama,, da kuma sanya hayaki maisa hawaye ga masu zanga zangar domin tsoratar wa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kano ta yi cikar farin dango
Yanzu haka sauran mutanan dake wurin sun zagaye Gawar ya rinyar domin jajantawa.
Wani shaidar gani da Ido, da ya bukaci jaridar The Nation ta sakaye sunan shi ya ce, lokacin da zanga-zangar ya yi kamari, sai yarinyar ta yi kokarin bude wani shago, inda nan ne harsashin ya same ta.
Sai dai jami’an yan sanda sun iso wurin da lamarin ya afku, kuma sun dauke gawar yarinyar.
Comments 2