Babbar Kotun masana’antu ta kasa ta sanya ranar Laraba 21 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan bukatar da gwamnatin tarayya.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Gwamnatin ta shigar da kara a gabanta kan kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) kan dogon lokacin da ta dauka tana yajin aiki.
KARANTA KUMA: Wata Kotu Ta Gayyaci Gwamnatin Tarayya Da ASUU
Mai shari’a Peter Hamman ya tsayar da ranar Litinin ne bayan da babban lauyan gwamnatin tarayya, Mista James Igwe, ya shigar da kara a gaban kotun.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa, Lauyan ya nemi kotu ta ba da umarnin hana ASUU ci gaba da yajin aikin da ke ci gaba da yi a fadin kasar.
A wani labarin kuma: Ummita Ta Nemi Shawarata Akan Auren Dan China Kafin A Kasheta – Aminu Daurawa
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa ya tattauna da Ummakulsum Buhari wadda aka fi sani da Ummita kan dangantakarta da dan kasar China da ya kashe ta a Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka kashe matashiyar a unguwar Janbulo da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano a daren ranar Juma’a.