Wani mutum dan Texas mai suna Giocchina Jack Poma, ya samu cikakken nishadi a wani gidan rawar fitar da tsiraici wanda diyarsa, Dina ta kai shi a cikin shagulgulan cikarsa shekaru 100, LIB ta ruwaito.
Yayin bayyana wa TMZ bayan shagalin ranar haihuwar tashi, Dina ta ce mahaifinta na matukar don abubuwa biyu a rayuwarsa, mata da albarkatun kirji.
KU KARANTA: Shekaru 11 na kwashe ina soyayya da yayana, shi ya rabani da budurci na, Budurwa
Ta ce rabon mahaifinta da zuwa gidan rawar nuna tsiraici tun yana saurayi, lokacin da yaje daren The Lodge Halloween.
Masu rawar sun yi mamakin yadda diyar da kanta ta kai mahaifinta wurin, amma ta ce musu dama ce ya samu, gara yayi amfani da ita yanzu da yake da rai.
Masu rawar sun nuna kauna ga Jack inda su ka ciyar da shi kayan dadi ciki har da kek din zagayowar ranar haihuwarsa, sannan sun ja hankalinsa bayan ganin ya yi matukar rikicewa.
Matar Jack ta rasu shekaru 12 da su gabata, tun bayan nan ne ya ci gaba da sharholiyarsa da wata budurwa, wacce a shekara da ta gabata ya rabu da budurwar.
N150,000 na ke samu kullum da sana’ar wankin mota, Dirarriyar budurwa
Wata ‘yar Najeriya mai matukar jajircewa akan aiki ta ta bayyana yadda a kullum take samun Naira dubu dari da hamsin sakamakon rike sana’arta da tayi, gospelarea.com ta ruwaito.
Duk da dai mutane da dama sun yaba mata akan dagewarta, sun kuma yi mamakin yadda yake samun N150,000 a ko wacce rana daga sana’ar wankin motoci.
Wasu kuma sun yarda da cewa har da yanayin sutturar da take sanyawa ne ya ke jan hankalin mutane wurin rububin kawo mata wankin motarsu.