Wata ‘yar Najeriya mai matukar jajircewa akan aiki ta ta bayyana yadda a kullum take samun Naira dubu dari da hamsin sakamakon rike sana’arta da tayi, gospelarea.com ta ruwaito.
Duk da dai mutane da dama sun yaba mata akan dagewarta, sun kuma yi mamakin yadda yake samun N150,000 a ko wacce rana daga sana’ar wankin motoci.
KU KARANTA: Ƴan uwa sun fi mutunta kuɗin da za ka aika musu akan ka wanke ƙafa ka ziyarce su, Budurwa
Wasu kuma sun yarda da cewa har da yanayin sutturar da take sanyawa ne ya ke jan hankalin mutane wurin rububin kawo mata wankin motarsu.
Kyakkyawar budurwar ta bayyana yayin da take wanke motoci kamar yadda ta saba sanye da wasu kaya masu fitar da duk wani lungu da sakon jikinta.
Mutane da dama na ganin tana samun wasu kudaden ne na daban sakamakon irin dirinta da kuma surarta.
Bayan shekaru 7 muna soyayya, Aliyu ya ɗirka min ciki kuma ya amshe kayan sa ranarsa, Budurwa
Wata budurwa mai suna daga wurin saurayinta mai suna Aliyu. Kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo wanda Rigar ‘yanci ta wallafa a shafinta na YouTube, shekarunta 20 da haihuwa kuma ta kwashe shekaru 7 su na soyayya da matashin har maganar aure ta shiga tsakaninsu.
Ta ce mahaifiyarta ta rasu kuma mahaifinta ba ya da lafiya, wannan yasa ta bayyana kanta gaban kungiyar tana neman a taimaka a kwato mata hakkinta.
A cewarta, matashin ya kawo kayan aurensa wanda daga bisani ya aika aka amsar masa bayan ya tilasta mata yin lalata da shi.
Comments 2