Wani dan Najeriya mai suna Mustapha Ahmad Junaid ya koka bayan rasuwar matarsa Fatim Zarah, a ranar da ya kamata su cika shekara daya da aure, LIB ta ruwaito.
Zahra wacce ta rasu da juna biyu a ranar Laraba, 7 ga watan Satumban 2022, bayan watanni 8 da aurensu.
KU KARANTA: ‘Yansanda sun ceto jariri da wasu ‘yanmata a Jihar Zamfara
Mustapha ya auri Zahra ranar 26 ga watan Nuwamban 2021 a Jihar Sokoto. Ya yi wallafa a Twitter ranar 26 ga watan Nuwamban inda yace har yau yana fama da radadin mutuwar Zarah.
Kamar yadda ya wallafa:
“Zahra, yau ce ranar da ya kamata aurenmu ya cika shekara daya amma bakya nan. Tun bayan rasuwarki babu ranar da ba na tunaninki.
“A wannan ranar shekarar da ta gabata mu na tare cike da farincikin kasancewa da juna. Lallai mutuwa gaskiya ce, na sani.
“Amma mun rabu cewa da kawar juna. Kin nuna min soyayya tsakani da Allah, amma Allah ya fi son ki kasance da shi. “
“Har yanzu ina tuna lokutan da mu ke tare. Kin kasance mace ta kwarai ga kowa. Na kwashe rayuwa ta ina fatan samun mace ta kwarai.
“Cikin sa’a na same ki. Amma kuma Allah be yi za mu dade tare ba. Ina fatan inda yake ya fi nan. Ina miki fatan Ubangiji ya yafe miki kurakurenki ya kuma ba ki Aljanna mafi daukaka.”
Budurwa ta tashi saurayi a Twitter bayan ya ce ya shirya aure amma babu matar aure
Wata mata a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba ta tashi wani matashi a Twitter yayin da ya bayyana cewa yana da zone amma bai samu budurwar da zai nemi aurenta ba, LIB ta ruwaito.
Abin ya fara ne bayan wani kwararre a harkar soyayya ya bukaci wadanda su ka yi aure da su gabatar da hotunan aurensu.
Sai dai matashin ya wallafa hoton zobe a hannunsa inda yace na aure ne amma har yanzu be samu matar da zai aura ba.