Wannan yana fitowa ne a wata sanar da kwamitin mai bawa sarkin Musulmai shawara kan harkokin musulunci ya fitar a jiya Alhamis.
Wannan ya biyo bayan sanarwar da Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta fitar a jiya Alhamis, inda kwamitin yace ba za a yi sallar Idi ba.
A sanarwar farko da fadar Sarkin ta fitar tace idan ya zama dole sai an yi jam’i musamman a jihohin da aka bayar da dama, to a yi sallolin a masallatan cikin unguwanni.
https://dimokuradiyya.com.ng/sultan-ya-umurci-alumman-musulmi-dasu-duba-jaririn-watan-ramadan/
A sanarwa ta biyu kuwa, fadar sarkin ta amince da a gudanar da sallar Idi a Masallatan Juma’a bisa jagorancin iyayen kasa Masu Unguwanni, Dagatai, Hakimai da kuma Limamai.
Fadar Sarkin ta kara da cewa an hana kananan yara da mata zuwa sallar Idin bana, sannan babu bukukuwan Sallah da kuma sauran al’adu da ake yi duk shekara da suka da hada da gaishe-gaishe.
Tun farko dai gwamnatin tarayya ta koka kam yadda wasu gwamnatocin jiha suka bada damar yin sallar Idi, inda Gwamnatin ta bayyana “Muna tufka ana warwara”.