A yammacin ranar Alhamis ne wata mai ciki da ba a bayyana sunanta ba ta rasu a hannun ‘Yan sanda a yayin da suke bincike akan hanyar ibiade dake Jihar Ogun.
Jaridar Tribune ta rawaito cewa mai cikin an dauke akan babur domin kaita asibiti amma sai jami’an ‘yan sanda suka tare su saboda sun karya doka wajen daukar mutum uku akan babur, ana wannan hali ne tace ga garinku nan.
Wasu matasa cikin fushi sun dauki gawar mai cikin zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta Abigi suna dora alhakin mutuwar matar akan jami’an ‘yan sandan.
https://dimokuradiyya.com.ng/dokar-hana-fita-yan-sanda-sun-cafke-mutum-325-a-legas/
Da aka tuntubi kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya musanta zargin da ake yiwa Jami’ansu cewa su suka yi sanadin mutuwarsu. Ya bayyana cewa jami’an suna bakin aikinsu ne domin tabbatar da dokar zaman gida dole, kuma sai suka ci karo da mai babur dauke da mutane uku.

“Jami’anmu basu da laifi, suna bakin aikinsu inda suka ga mutane uku akan babur wanda ya saba da dokar da gwamnati ta bayar na daukar mutane biyu kadai domin bada tazara”.
“An tsayar da su aka tambaye su mene en dalilinsu na kin zaman gida, suka bayyana cewa suna dauke da mai ciki ne kuma zasu kaita asibiti domin haihuwa, kuma nan take aka ce su wuce”.
Daga bisani dai manya sun shiga cikin lamarin domin kawo karshen tada jijiyar wuya dake faruwa tsakanin jami’an’yan sanda da wasu matasan yankin.