Hausawa dai sun ce idan ajali yayi kira a tafi ko babu ciwo. Wani matashi mai suna Ibrahim ya amsa laifin kashe dan uwansa ‘Kadade’ bayan da ya shiga hannun Jami’an’yan sanda.
Jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar cafke matashin mai shekaru 20 da haihuwa a wani sumame da suka kai a kauyen ‘Kateri’ dake jihar Kaduna.
Ibrahim tare da mamacin dan uwan nasa haifaffun kauyen Amana Maikasuwa ne dake karamar hukumar Igabi a jihar ta Kaduna.
Bayan samun rahotannin da ‘yan sanda suka samu ne tare da hadin guiwar ‘Yan Kato-da-gora suka kai sumamen inda suka yi nasarar cafke matashin tare sa wani mai suna Amadu dan shekaru 22 da haihuwa.
Yayin da yake tattaunawa da manema labarai, Ibrahim yace yana tare da wasu gungun masu yin fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma kwacen Shanu.
Ya kara da cewa shi ne ya dauko hayar wasu tare da taimakon wani dan kungiyar su domin su kashe ‘Kadade’ saboda mahaifinsu yafi kaunarsa sama da shi.
https://dimokuradiyya.com.ng/ajali-mai-ciki-ta-mutu-a-hannun-yan-sanda/
Ya ce mahaifinsu ya sayar da shanu wanda kudinsu ya kai kimanin Miliyan daya da dubu dari bakwai (1.7M) kuma aka bawa dan uwana ya ajiye kudin.
Matashin ya kara da cewa wannan dalilin ne yasa shi fusata, inda ya tunkari wani abokinsa mai suna Amadu domin ya taimaka masa wajen kashe dan uwan nasa.
Amadu ya taimaka masa suka dauko hayar Kiri Jumare, Auwalu, Nakaduwa sa kuma Yellow, domin aiwatar da aikin da aka dauko su.
” A daren ranar da misalin karfe 12:30 na dare, wajen mutane 5 suka hauro gidanmu sai suka kwankwasa min kofar dakina wato alamun sun karaso. Da suka bincika gidanmu suka samu dan uwana nan take suka kashe shi. Ni kuma na dauka hakan zai sa mahaifinmu ya dawo da komi wajena”.
Ibrahim ya kara da cewa bayan sun kashe shi suka hadu da daji inda suka shaida masa sun samu kudade Naira dubu 300, shi kuma ya karbi dubu 100 saboda shi ne wanda ya aikin.
Daga bangarensa kuwa Amadu, ya bayyanawa jami’an’yan sanda cewa tun yana dan shekaru 15 mahaifinsu ya kore sa daga gida saboda ba zai iya rike shi sakamakon yara da yawa da ya haifa. Kuma ya fara yiwa wani Mutum mai suna Sani kiwo da nufin zuwa wani lokaci a sallame shi. Ana wannan hali ne wani abokinsa mai suna Haruna ya fara nuna masa hanyar da ake samun kudi ba tare da an wahala ba. Daga nan ne Amadu ya fara sayar da shanun mai gidansa ba tare sa ya sani ba.
‘Yan sanda sun sanar da cewar sun kai sumamane ne bayan da suka samu rahoton cewa akwai masu laifi a yankin, kuma wanda ake zargin sun amsa laifuka da suka hada sa fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma satar Shanu.