Gwamnatin tarayya ta ce aikin layin dogo da ake kokarin samarwa daga nan Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar zai taimaka wajen bunkasa kasuwanci da harkokin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Daraktan yada labarai na maaikatar sufuri ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar tare da rabawa manema labarai a birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Sojoji sun lalata wasu matatun mai 39
A cewarsa Ministan sufuri Muazu Sambo shine ya tabbatar da hakan yayin sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Najeriya da jamhuriyar ta Nijar kan aikin layin dogon.
Layin Gogon dai zai fara ne daga nan Kano a Najeriya zuwa Maradi dake jamhuriyar Nijar, kuma zai taimaka wajen karfafa shirin nan na kasuwanci ba tare das hinge ba tsakanin kasashen afrika.
A nasa bangaren ministan sufurin Nijar Alma Umaru ya ce samar da layin dogon zai taimaka wajen karfafa alakar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu.
Punch ta rawaito cewa aikin zai kuma taimaka wajen samar da ayyukan yi, ga al’ummar kasashen biyu baki daya.
A wani labarin kuma: Idan Barcelona Ta Kira Ni, Zan Koma, Ai Kungiyata Ce —Pep Guardiola
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya kare matakin Mikel Arteta na yin watsi da tsohon mukaminsa na mataimakinsa a Etihad domin karbar jagorancin kungiyar Kwallon kafa ta Arsenal. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Guadiola ya ce ko shi ne ba zai dau wani mataki da ya sha banban da wanda Arteta ya dauka ba musamman ma idan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce ta kira shi da ya koma.