Ba tare da jin wata kunya ba, wani mutum mai shekara 55 a duniya, mai suna Rusengamihigo Jean Marie Vianney, ya koma makarantar firamare.
Mutumin wanda yanzu haka aka sanya shi a aji biyar, yana koyon karatu tare da ƴara waɗanda sa’ar jikokin sa ne. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya Real Madrid ke shirye-shiryen korar kocin ta
Vianney wanda ya daina zuwa makaranta yana aji shida, ya bayyana cewa ya samu ƙwarin guiwar komawa makaranta ne saboda gwamnati.
“Na fara makaranta, amma daga baya na daina zuwa. Daga baya gwamnati ta ƙarfafawa mutane da dama guiwa su koma makaranta.”
“Ina daga cikin mutanen da suka koma makaranta bayan na daina zuwa lokacin ina aji shida.”
Shekarun baya lokacin da Vianney yake makaranta ana koyawa yara karatu ne da yaren French, hakan ya sanya yanzu yake shan wahala saboda yanzu da Turanci ake yi.
A wani bidiyo da majiyar mu ta sanya, ya nuna wani lokaci na musamman da matarsa ta shirya shi sannan tayi masa addu’a kafin ya tafi makaranta.
Matar Ta Aure Ta Raka Mijinta Wajen Na Maggi, Ta Zage Damtse Anyi Da Ita
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure tayi wani abin da ya ɗauki hankulan mutane da dama.
Wata matar aure ta zama abin magana a yanar gizo, saboda ta raka mijinta wajen aikin sa na aikin famfo.
Matar auren ta sanya bidiyon ne a manhajar TikTok domin nuna lokacin da, ita da mijinta suka yi wani aikin kwangila tare.
Sun yi aiki tare inda suka kammala kwangilar cikin lokaci. Kwangilar da suka yi ta ƙunshi sanya babban tankin sama.