Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam (CSOs), sun buƙaci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauya dokar da ta tilasta sanya jami’in tsaro su shugabanci hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC).
Shugaban ƙungiyar Transparency Advocacy for Development Initiative (TADI), Yomi David, ya yi kiran a Abuja, inda ya ce sauya dokar kafa EFCC ne kaɗai zai kawo nasara a ƙudirin Buhari na yaƙar cin hanci da rashawa a Najeriya.
Ya yi kira ga Shugaban ƙasar da ya gaggauta umurtar Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya sauya dokokin kafa EFCC na 2003, musamman wadda ta ce, “Dole a damƙa shugabancin hukumar a hannun jami’in tsaro (tsoho ko mai ci).
“Ya kamata Shugaba Buhari ya hana ’yan sanda da gurbatattun ’yan siyasa mulkar hukumar.
https://dimokuradiyya.com.ng/an-saki-tsohon-shugaban-efcc-ibrahim-magu/
“Ya kawo ƙwararru masu ilimin bincike na ƙarni na 21, waɗanda suka yi suka san kan fasahar binciken kadarori da gano su, da kwato su da binciken masu laifi da kuma kwarewa wajen gurfanar da ɓarayi a gaban kotu.
“Muna rokon Shugaban Ƙasa ya aiwatar da shawarwarinmu domin ya tabbatar da cewa a shirye yake ya gyara hukumar” cewar shugaban ƙungiyar.
Ya ce hakan shi zai bawa mutane ƙwararru, masu gaskiya, marasa tabo damar shugabantar hukumar.