Femi Falana SAN ya kai ƙarar gwamnatin jihar Kano da ta tarayya a gaban hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta Afrika da ke Banjul, babban birnin ƙasar Gambia, game da hukuncin kisan da aka yankewa wani mawaƙin da ya yi ɓatanci ga Annabi. S. A. W.
Da ma dai Falana, wanda babban lauya ne kuma mai rajin kare haƙƙin bil-Adama, ya ɗaukaka ƙara don ƙalubalantar hukuncin da aka yankewa Sharif Yahaya Sharif, matashin da aka tuhuma da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW) a Kano.
A saƙon da ya aike mai ɗauke da kwanan watan ranar 8 ga watan Satumba, Falana ya nemi hukumar da ta shiga lamarin, saboda a cewarsa an dannewa matashin haƙƙinsa yayin da ake neman zartar masa da hukuncin kisa.
“Na rubuto muku wannan saƙo a madadin Sharif Yahaya Sharif don neman hukumar ta yi la’akari da wannan buk5ata cikin gaggawa.
“Na gabatar muku da buƙatar ne tare da isar da saƙo a madadin Sharif Yahaya Sharif wanda aka yanke masa hukuncin kisa saboda aikata saɓo a jihar Kano ta Najeriya”, cewar Falana.
Fitaccen lauyan ya ce duk da an ɗaukaka ƙara, muddin hukumar ba ta yi gaggawar shiga lamarin ba, to kuwa babu tabbacin za a yi wa matashin adalci domin babu wata alama da ke nuna za a fasa zartar da wannan hukunci.