Gwamnatin tarayya ta roƙi ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta ƙasa JOHESU da ta janye yajin-aikin gargaɗi na sati ɗaya da ta shiga.
Ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin lokacin da kwamitin yaƙi da cutar Korona na ƙasa ke ƙarin haske dagane da cutar a Abuja.
“Zan yi amfani da wannan dama na roƙi JOHESU ta zan ye yajin-aikin da ta shiga a zo a tattauna”.
“Yajin-aikin ma’aikatan lafiya ba abinda zai haifar face jefa rayuwa mutane a cikin haɗari”.
https://dimokuradiyya.com.ng/likitoci-na-barazanar-shiga-yajin-aiki-a-ranar-litinin/
“A wannan yanayi da ake ciki na yaƙi da wannan annoba a duniya, babu abinda Najeriya ke buƙata face haɗin gwiwar dukkanin ma’aikatan lafiya”.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa shugaban ƙungiyar Dakta Biobelomoye Josiah yace, dole ne su ma a basu dama a saurare su kamar yadda aka saurari ƙungiyar Likitocin cikin gida NARD.
JOHESU, ƙungiya ce mai zaman kanta kuma wani tsagi na ma’aikatan lafiyar ƙasar, ta ce ita ma dole ne a saurareta tare da bata dukkanin haɗin kai da kuma abinda ya kamata.