Fitaccen fasto Gerald Johnson, wanda ya mutu na wucin gadi ya janyo cece-kuce kala-kala a kafafen sada zumuntar zamani, Legit.ng ta ruwaito.
KU KARANTA: Kun ji kunya: Fasto ya harzuka kan masu bada sadakar N100
A cewarsa kamar yadda ya bayyana a shafinsa na TikTok, bayan ya yi mutuwar wucin gadi sakamakon bugawar da zuciyarsa ta yi a Fabrairun 2016, ya ji wani abin ban mamaki.
Ya ce ya ji yadda azabar wuta yake don haka ba zai taba yi wa wani fatan shiga wutar ba. Sannan akwai wani yanki da ke wuta wanda ‘yan wuta ke sauraron wata wakar da ke duniya mai suna Umbrella ta mawakiya Rihanna da kuma Don’t Worry Be Happy ta Bobby McFerrin.
Na san cewa a duniya, an yi wakoki da yawa kuma yawanci shaidanu ne suke kirkirarsu.
Kuma wani lokaci akwai masu shayeshayen da ke buguwa don su kirkira waka a duniyar nan.
Sannan faston TikTok din ya ce ya ga wani mutum a wani yanayi a cikin wuta. Ya kara da cewa:
“Daya daga cikin abubuwan da suka ba ni mamaki su ne yadda aka babbake wani mutum da kai kan sa zuwa kafafu.
”Abinda ma ya fi ban tsoro shi ne yadda aka daure masa wuya da kaca kamar kare. Kuma akwai wani shaidani da ke rike da kacar.”
Saka rigar bacci ɓata lokaci ne saboda zuwa safe za ki tsince ta a ƙasa, Fasto ga matarsa
Wani fasto da ke Jihar Akwa Ibom, Ab Isong ta sanar da matarsa, Emem Isong cewa ta dena wahalar da kan ta saka rigar bacci da dare, LIB ta ruwaito.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce bata lokacinta take yi saboda dole ne a cire ta cikin dare.