Babban Surveyor Janar na Tarayyar Najeriya, Abudulganiyu Adebomehin, ya yi gargadin cewa Abuja, babban birnin Najeriya, na kara zama wani matsuguni na nutane ba kamar yadda aka sanshi a mataayin birni mai daraja ba.
Adebomehin ya yi magana ne a ranar Talata yayin da yake gabatar da jawabi a gaban kwamitin majalisar wakilai kan raya birane da tsare-tsare na yanki.
Karanta nanRanar 15 Ga Watan Disamba Za A Baiwa Daliban Jahar Kano Hutun Makaranta-Kwamishina
Ya bayyana cewa wannan ci gaban ya biyo bayan rashin bin tsarin babban birnin da mutane masu yin gine gine ba suyi.
Abuja tana da saurin juyewa zuwa ga marasa galihu yanzu, yallabai,abu daya ne za ka bukaci ka yi magana da masu kula da Abuja. Ina ganin ya kamata mu kare Abuja domin wasun mu su zauna a Abuja bayan mun yi ritaya.
Idan muka yanke shawarar cewa muna son zama a Maitama a yau me ya sa muke ƙaura zuwa Maitama,ba wani abu bane illa saboda yanayin tsaro da tsarin da unguwar ke dashi
Za mu iya yanke shawarar mayar da Lugbe kamar Maitama da sauransu in ji shi.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin, Awaji-Inombek Abiante, ya ce daukacin kasar na saurin rikidewa ta koma cikin wani mawuyacin hali.
A wani labarin kumaRashin Iya Mulki Ne Ya Janyo Yan Majalisu 27 Barin PDP-Jam’iyar APC Reshen Jahar Ribas
Ya kuma jaddada cewa dole ne a dauki kwararan matakai domin sauya lamarin.
Dan majalisar ya kara da cewa, kwamitin ya kira taron ne domin a samar da manufa guda daya tak a kan tsare-tsare na birane domin kaucewa duk wani abu da kasar nan ta koma cikin wani mawuyacin hali.
Taron ya samu halartar masu tsara birane da yankuna daga jihohi daban-daban na Nijeriya inda kowa a cikinsu ya tofa albarkacin bakinsa akan yanayin da babban birnin tarayyar yake ciki.