A makon nan da muke shirin bankwana da shine sarauniyar Burtaniya Elizabeth II ta mutu, wanda mutuwarta zai haifar da sauye sauye da dama a kasar.
Sauyin Da Zai Faru Ga Kudin ƙasar.
Zai fuskanci sauyi ta yadda yake a yanzu da kuma zuwa lokacin da mulkin Sarki Charles III zai kan kama.
Yanzu haka dai hoton Elizabeth ne a jikin kudin, kuma sannu a hankali za a fara buga sabbin kudi wadanda zasu fito da Sarki Charles III maimakon na mahaifiyarsa.
KARANTA ANAN: Har Yanzu Boko Haram Na Rike Da Yan Matan Chibok 98 – Rundunar Soji
Bisa tsarin kasar duk Sarkin dake kan mulki to kudin ƙasar yana dauke ne da hotonsa, idan ya mutu wanda ya gaje shi sai shima hotonsa ya maye gurbin nasa ko nata.
Bayan haka sai kuma?
Sauran abubuwa da suka haɗar da Fasfo, Satamfi, Kakin Yan Sanda, na sojoji duk suma za a cire hotunan Elizabeth II, tare da maye gurbin wajen da
hoton sarki Charles III.
Da sauran abubuwa da za a sauya misali taken kasar shima sai na gyara shi daga ‘God Save the Queen” ya koma anan fadar ”God Save The King.”
A wani labarin kuma: Sarauniya Elizabeth II Ta Taimaki Najeriya Lokacin Yaƙin Basasa – Buhari
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ce kasar Birtaniya a karkashin marigayiya Sarauniya Elizabeth ta goyi bayan Najeriya a lokutan da masifu da dama suka tunkaro ta.
Ya ce Birtaniya a lokacin yakin basasa tsakanin 1967 zuwa 1970 ta goyi bayan hadin kan Najeriya, inda ya ce Sarauniyar ta ziyarci kasar sau biyu kafin rasuwarta.