Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ce kasar Birtaniya a karkashin marigayiya Sarauniya Elizabeth ta goyi bayan Najeriya a lokutan da masifu da dama suka tunkaro ta.
Ya ce Birtaniya a lokacin yakin basasa tsakanin 1967 zuwa 1970 ta goyi bayan hadin kan Najeriya, inda ya ce Sarauniyar ta ziyarci kasar sau biyu kafin rasuwarta.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga babbar jami’ar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, a gidanta da ke Abuja ranar Asabar.
KARANTA ANAN: PDP Ta Sake Rasa Wani Jigo Bayan Ya Kara Mai Zuwa Jam’iyyar APC
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya wakilce shugaban kasar.
Buhari ya kara da cewa, “Shugabar kasashen duniya da dama wadanda Burtaniyan ta Muljam, wato shugabar Commonwealth za a dade ana tunawa da ita, da kuma irin tarin gudunmawar da ta bayar a bangarori da dama.
Marigayiyar Ta ziyarci Najeriya sau biyu; na farko a shekarar 1953 ta kwashe kimanin kwanaki 20 tana ziyartar garuruwa daban-daban, na biyu kuma a shekarar 2003 lokacin shugaban kasa Olusegun Obasanjo,” inji Buhari
Najeriya ta tabbatar da cewa za a bude wani kundin ta’aziyya na Marigayiyar a ofishin jakadancin kasar dake Abuja, daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Satumba da kuma ranar 19 ga wata da karfe 11 na safe zuwa 3 na rana a kullum.
A wani labarin kuma: Sojoji Sun Hallaka Wanda Ya Kitsa Harin NDA Ta Kaduna
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama a kewayen babbar unguwar tollgate a karamar hukumar Chikun ta jihar.
Kwamishinan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce daga cikin ‘yan bindigar da sojojin suka kashe, akwai Musti, wanda ya jagoranci wani mummunan hari a shekarar da ta gabata a Kwalejin horas da sojoji ta Najeriya dake Kaduna.
Comments 1